27 Yuli 2019 - 06:49
Zarif Ya Fara Ziyarar Aiki A Kasar Senegal

A daren jiya Laraba Ministan harakokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran Muhamad Jawad Zarif ya fara ziyarar aiki a kasar Senegal

(ABNA24.com) Kamfanin dillancin labaran Irna ya bayar da rahoton cewa, a jiya Laraba ministan harakokin wajen jamhuriyar musulinci ta Iran ya sauka a birnin Dakar na kasar Senegal, inda ake sa ran zai gana da takwaransa na Senegal da kuma Shugaban Majalisar dokokin kasar.

Tun a ranar 13 ga watan Yuli ne Zarif ya bar birnin Tehran zuwa birnin New York na Amurka da nufin halartar taron manyan jami'ai na kwamitin tattalin arziki da zamantakewa na Majalisar Dinkin Duniya.

A yayin wannan ziyara, Zarif ya tattauna da kafafen yada labarai na CNN da BBS, kuma bayan jawabi da ya gabatan a kwamitin tattalin arziki da zamantakewa na MDD, Ministan harakokin wajen Iran din ya gana da Sakatare janar na Majalisar António Guterres musaman ma kan rikicin da ya kunno kai a yankin gabas ta tsakiya da kuma jingine wani bangare na yarjejeniyar nukiliya da kasar Iran ta cimmawa da manya kasashen biyar na Duniya gami da kasar Jamus, tare kuma da bayyana cewa rike jirgin ruwan dakon man Iran da kasar Birtaniya ta yi ya sabawa dokokin kasa da kasa.

Kafin kasar Senegal dai, Zarif ya ziyarci kasashen Venezuela da Nicaragua da Bolivia inda ya tattauwa da hukumomin kasashen.



/129