Babbar kotun dake Jihar Kaduna ta bayar da Umarnin aci gaba da tsare tsohon Gwamnan Jihar Kaduna a karkashin inuwar jam'iyyar PDP Muktar Ramalan Yaro.
Haka kuma kotun ta kuma bayar da Umarnin tsare tsohon Ministan Lantarki na Jiha Nuhu Wya da tsohon sakataren Gwamnatin Jihar Kaduna Hamza Ishaq Dan mahawayi da kuma tsohon ciyaman na Jam'iyyar (PDP)Haruna Gaya.
Kotun kolin Jihar Kaduna tana tuhumar tsofaffin shugabanin da laifukan da suka shafi cin amanar kasa wawushe dukiyar Al'umma da kuma aikata almundahana.
Mai Shari'a Mohammed Shuaibu shiya bayar da Umarnin tsare su bayan karbar rahoton hukumar (EFCC).
Duk da dai lauyan Muktar Ramalan Yaro ya bukaci a bashi belin tsohon Gwamnan domin ya tafi dashi gida,sai dai alkalin yayi burus da bukatar haka.
Alkalin kotun ya bayar da umarnin tasa keyar tsohon Gwamnan da mutun uku da ake tuhumarsu zuwa gidan yari har zuwa Ranar Alhamis mai zuwa.
31 Mayu 2018 - 15:01
Lambar labari: 895716
Wata Babbar Kotu ta Bayar da umarnin Garkame tsohon Gwamnan jahar Kaduna a Gidan Yari tare da mutun uku: