Wani da ya tsira da ransa a rikicin, Sa'adu Mogoggo ya shaida wa manema labarai cewa, an kai wa gidansa hari, in da aka kashe ‘yan uwansa biyu a yammacin ranar Asabar tare da sace shanunsu, yayin da ya dora laifin farmakin kan wasu ‘yan tawayen Mambila.
Rahotanni na cewa, har ya zuwa jiya Lahadi, an ci gaba da fama da tashin hankalin da wasu ke alakanta shi da rikicin Fulani makiyaya da ‘yan kabilar Mambila.
Abdu Gagarau, daya daga cikin mazauna yankin ya ce, tun a ranar Alhamis da ta gabata ne aka fara tashin hankalin, kuma ya tabbatar da mutuwar mutane akalla 20 tare da fadin cewa, ‘yan kabilar ta Mambila sun sace shanu sama da 300.
Gagarau ya ce, Mambilawa sun yi kaurin suna wajen kai wa sauran kabilu farmaki a Taraba da suka hada da Fulani.