Shugaban yace yarjejeniyoyin, zasu bai wa kasashen damar bunkasa harkokin kasuwanci da kuma kare masu zuba jari.
Erdogan yace Turkiy na kallon Algeria a matsayin kasar da ke kan gaba wajen samun kwanciyar hankalin siyasa da kuma habakar tattalin arziki a Afirka.
Ana saran shugaban ya ziyarci kasashen Mauritania, Senegal da kuma Mali.