A cikin wata sanarwa da ta fitar , hukumar zaben kasar Liberia ta tabbatar da cewa Tsohon shahararren dan kwallon kafa ne na Duniya wato George Weah shi ne ya lashe zaben shugaban kasar da kashi 61,5% na kuri'un da aka kada yayin da abokin hamayarsa mataimakin shugaban kasa mai ci mista Joseph Boakai ya samu kashi 28,8.
Jim kadan bayan samun labarin nasarar ta Mista Weah, magoya bayansa suka fara bukukuwan nuna murnarsu a babban birnin kasar na Monrovia.
A ranar 22 ga watan janairu na shekara mai kamawa ne ake sa ran za a rantsar da sabon shugaban kasar ta Liberia.
A yayin yakin neman zabe, Mista George Weah ya yi alkawarin farfado da tattalin arzikin kasar ta hanyar yaki da barnar dukiyar kasa