8 Satumba 2017 - 19:25
Aya. Muwahhidi Kermani:Kasashen Duniya Basa Ganin Musulmai Zasu Iya Tashe Don Kare Yan'uwansu Na Myanmar

Limamin da ya jagoranci sallar Jumma'a a nan Tehran, Aya. Muwahhedi Kermani a cikin khubobinsa na Jumma'a ya bayyana cewa kasashen duniya basa zatun musulmi suna iya tashi don taimakawa yan'uwansu a kasar Myanmar wadanda sojojin kasar da kuma mabiya addinin Buza suke azbtarwa.

Aya. Kermani ya kara da cewa tun ranar 25 ga watan Augustan da ya gabata ne sojojin kasar Myanmar da mabiya addinin Buza suke dirar mikiya kan musulman kasar Myanmar wanda ya zuwa yanzu sun kashe fiye da mutum dubu daga cikinsu sannan wasu kimani dubu 100 sun gudu daga kasar don tsira da ransu.

Limamin ya kara da cewa tun shekara ta 2012 ne gwamnatin kasar Myanmar ta fara shirin shirin  kuntatawa musulman kasar miliyon guda yan kabilar Rokhinga kuma a jihar Rokhin. Gwamnatin Myanmar bata amince da kasashen cewa yan kabilar Rokhinga a matsayin yan kasa ba, don haka ta haramta masu dukkan hakkin dan kasa.

A wani bangaren limamin ya yi maganar kisan mutanen Yemen wanda sarakunan kasar saudia suke ci gaba da yi, ya kuma kara da cewa mahukuntan kasar ta saudia basu damu da addini ba ko kadan ballantana su kula da ka'idojinsa.

Dangane da bukatar Amurka na hukumar IAEA ta bincike wurare ajiye makamai na kasar Iran kuma, Aya. yace gwamnatin kasar Iran ba zata taba amincewa da haka ba. Banda haka ya ce gwamnatin JMI ta bada hadin kai fiye da kima ga hukumar a binciken cibiyoyin Nukliyar kasar kamar yadda tayi alkawari, amma batun binciken rumbunan ajiye makaman kasar hakan ba zai samu ba.288