13 Agusta 2017 - 11:39
Ministan Yada Labaran Nigeriya da Femi Adesina da Malam Garba Shehu Sun Ziyarci Shugaba Muhammadu Buhari a Ingila

Femi Adesina a wata takarda da ya fitar yau Asabar,12 ga watan Agusta 2017,ya bayyana cewa yana cikin tawagar Ministan Yada labarai,Mr Lai Muhammad da suka kai wa Shugaba Muhammadu Buhari ziyara a Ingila. A lokacin da Shugaba Buhari yake masu bayani dangane cigaban da ya samu dangane da lafiyarsa ya bayyana masu cewa: "Alhamdulillah,na samu sauki sosai dangane da rashin lafiya ta,kuma ina son in dawo gida,amma dai na ga ya fi dacewa in bi umurnin likita na,ba wani ba saboda shike da cikakken masaniya dangane da abinda ya kamata na yi."in Shugaba Buhari. In ba a manta ba,Shugaba Buhari ya kwashe fiye da kwanaki 90 a Ingila domin ganin likitansa,wanda wannan ya haifar da taqaddama tsakanin mutanen Nigeriya.

London

London

London