Kamar kowace shekara a karshen Juma'ar watan Ramalana mai alfarma; al'ummar Iran sun fito kwansu da kwarkwatansu, inda suka gudanar da zanga-zangar ranar Qudus ta duniya da nufin jaddada goyon bayansu ga al'ummar Palastinu da ake zalunta su na rera taken tofin Allah tsine kan yahudawan sahayoniyya 'yan kaka gida da kanwa uwar gami Amurka tare da jaddada bukatar kawo karshen duk wata bakar siyasar zalunci kan al'ummar Palastinu.
Har ila yau masu zanga-zangar sun yi ta rera taken neman hadin kan al'ummar musulmin duniya tare da kawo karshen duk wata siyasar bakanta sunan addinin Musulunci da wasu jama'a ke yi ta hanyar kai hare-haren ta'addanci.288