Zariya, Kano, Potiskum da Lafiya.
Taron ranar tunawa da shahidai na Harkar Musulunci a Nigeria, taro ne da ake gabatarwa a ko wacce shekara a dai ranar da ake tunawa da shahadar Babul Hawaeej Imam Musa Kazeem[AS] watau ranar 25 ga watan Rajab mai alfarma.
Babban makasudin tarurrukan shine don tunawa da gwarazan mu Shahidan mu wadanda suka bada jinenen su fisabilillah, sannan da kula da abin da suka bari a baya na 'ya'ya da iyalai.
A shekarun baya bayan nan tun bayan waki'ar Gyallesu ana raba tarurrukan ne a gudanar da su a garuruwa daban daban.
Malam Yakubu Yahaya Katsine shine babban bako mai jawabi a taron an Kano, Malam Abubakar Nuhu T/Mafara kuma shi ya gabatar da na Potiskum, kamar yadda Malam Adamu Tsoho Jos ya gabatar da jawabi a na garin Lafiya, sannan kuma Malam Kasimu Ummar Sakkwato ya gabatar a taron na Zariya.
Dukkanin su an gabatar da su lafiya.288