28 Maris 2017 - 14:22
Mayakan boko haram sun sace mutane 10 a Borno

Jami’an tsaro a jihar Borno, sun ce mayakan Boko Haram sun kutsa cikin karamar hukumar Konduga, inda suka sace mutane goma.

Kwamandan hukumar jami’an tsaron farin kaya ta NSCDC na Borno, Ibrahim Abdullahi, ya ce mayakan sun shiga karamar hukumar ce a kan Babura 10, inda suka sace mata hudu da matasa 6 daga kauyen Kalari da ke karamar hukumar ta Konduga.

Abdullahi ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN cewa, ‘yan kungiyar ta boko haram, sun kuma kutsa kauyukan Mittiri, Akalli, da kuma Arribbari da ke karamar hukumar ta Konduga.

Kwamandan ya bukaci, jama’a da su cigaba da kasancewa cikin kula a kowane lokaci, kasancewar rahotannin sirri da ke hannunsu ya nuna cewa, mayakan na boko haram da suka rage, bayan tarwatsa su da sojin Najeriya suka yi, suna fafutukar tilastawa wadanda suke sacewa, bin umarnin kungiyar wajen kai hare haren ta’addanci.288