A cikin sakon bidiyon, shekau ya ce sun gwabza fada da sojoji a kan iyakar kamaru tare da karyata ikirarin gwamnatin kasar da ta ce ta kashe mayakan shi 60 cafke wasu 20 da kuma kubutar da mutane sama da 5,000 a makwannin da suka gabata.
A hoton bidiyon na tsawon minti 27 , shugaban na Boko Haram ya ce yana nan garau tare da karyata ikirarin an raunana shi.
Sai dai kuma yanayinsa da babatunsa ba kamar yadda ya saba ba, a hoton bidiyon da ya fito tare mayakansa biyu a bayansa sun rufe fuska rike da makami.
Wannan ne karon farko da shekau ya fito tun fitowarsa a hoton bidiyo a watan Disemban bara lokacin da sojojin Najeriya suka ce sun kakkabe ‘yan Boko Haram a dajin Sambisa.288