Sanarwar ta ce Sarkin na Morocco ya tambayi lafiyar Buhari tare da bayyana gamsuwarsa.
Shugabannin sun kuma tattauna akan halin da ake ciki ga aikin shinfida bututun da zai ratsa Morocco zuwa kasashen Turai daga Najeriya.
Sannan Sarkin ya sanar da Buhari game da bukatar Morocco na shiga kungiyar kasashen yammacin Afrika ECOWAS tare da mika godiya ga goyon bayan da suka samu na dawo da kasar a Kungiyar Tarayyar Afrika.288