Dubban mutane ne ake sa ran za su halarci bikin ciki har da shugabanin wasu kasashen Duniya.
A watan da ya gabata ne aka rantsar da shugaban a ofishin Jakandancin Gambiya da ke kasar Senegal bayan da tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh ya ki sauka daga mulki duk da kayen da ya sha a zaben shugabancin kasar da aka gudanar.
Daruruwan al’ummar Gambiya sun tsere daga kasar saboda kaucewa tashin hankali sakamakon rikicin zaben kasar da ya biyo bayan kememen da Jammeh ya yi akan karagar mulki.
Daga bisani dai kasashen Tarrayar Afrika sun yi nasarar warware rikicin cikin ruwan sanyi inda har suka yi nasarar lallamar Jammeh har ya amince da barin kasar zuwa Equatorial Guinea.