Jaridar Dailytrust ta Nigeria ta nakalto mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin watsa labarai Garba shehu yana fadar haka a safiyar yau Talata a hirar da yayi da tashar television ta Chennel.
Shehu garba ya kara da cewa shugaban bai ji dadin dadewar da yayi a kasashen waje ba don haka zai dawo gida tsammani daga yau Talata. Dangane da rashin lafiyarsa kuma Shehu garba ya ce bai san cewa ko shugaban ya karbi dukkan sakamakon gwaje gwajebn da aka yi masa ba.
Sai kuma dange da tattaunawar shugaban da shugaban kasar Amurka shehu garbe ya ce bai kamata a watsa sautin tattaunawan shuwagabannin biyu daga ko wane bangare don hakan ya sabawa tsarin diblomasia ta kasa da kasa, sai dai abinda ya bayyana a cikin tattaunawar shi ne cewa trump ya gaiyyaci buhari zuwa Amurka.288