Mai magana da yawun shugaban kasar Garba Shehu ya ce, an cafke mutane 11 da ke tafiyar da wannan yaudara ta ma’aikatan boge tare da mika su ga hukumar yaki da rashawa ta kasar, EFCC.
Shehu ya ce, kafin gwamnatin Najeriya ta kafa kwamitin bincike a cikin watan Fabairun da ya wuce domin tantance adadin ma’aikata na gaskiya, ana biyan albashin Naira milyan dubu 151 a kowane wata, to amma bayan gano ma’aikatan na boge albashin ya dawo zuwa Naira milyan dubu 138, abin da ke nufin cewa, gwamnatin na tsimin Naira biliyan 13 a kowane wata a yanzu.
Tuni dai gwmnatin Buhari ta kudiri aniyar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa.288