Rahotanni daga jihar Bornon sun bayyana cewar babban hafsan sojin Najeriya Laftanal Janar Tukur Yusuf Burutai ne ya jagoranci bikin sake bude hanyoyin wadanda aka rufe su na tsawon lokaci saboda hare-haren da 'yan Boko Haram suke kai wa mutane masu bi ta wajen.
Rahotannin sun ce a yayin wannan bikin dai wanda gwamnatin jihar Bornon ma Kashim Shattima na wajen, an bude hanyoyin Maiduguri-Mongunu-Baga da kuma Maiduguri-Damasak.
A ranar Asabar din da ta gabata ce dai shugaban Nijeriyan Muhammadu Buhari ya sanar da kwace babbar tungar 'yan Boko Haram din da ke Dajin na Sambisa wanda ake ganin hakan a matsayin wata gagarumar nasarar da sojojin Nijeriyan suka samu kana kuma alama kusan ta karshe ta kawo karshen 'yan Boko haram din.288