Wannan na zuwa ne sa'o'i kadan bayan da wasu shugabannin kasashen Afirta ta Yamma suka isa kasar domin shawo kan Shugaba Yahya Jammeh ya amsa kayen da ya sha a zaben.
Mista Njai ya shaida wa BBC cewa jami'an tsaron sun kuma umarce shi da ya bar ofis dinsa.
"A yanzu na bar ofis na koma gida... da alama suna kar bar umarni ne daga wani wuri,"in ji shi.
A sakon da ya aike a shafinsa na Twitter, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce za su nemi Mista Jammeh ya mutunta tsarin mulki, kuma ya kaucewa abin da zai haifar da tashin hankali a kasar.
Shugaban kungiyar ta Ecowas, Marcel de Souza, ya yi barazanar cewa za su yi amfani da karfi idan Mista Jammeh ya ki mutunta kundin tsarin mulkin kasar.
Zababben shugaban kasar Adama Barrow, wanda ya kayar da Mista Jammeh a zaben na 1 ga watan Disamba, ya nemi taimakon kasashen duniya.
A watan gobe ne ya kamata a rantsar da shi a kan karagar mulki.
Mista Buhari ya ce Shugaba Jammeh ya yi musu kyakkyawar tarba a ganawar da suka yi da shi.
Shugabannin sun gana ne a sirri na tsawon sa'a guda.
Babu wani cikakken bayani kan abin da suka tattauna ko matsayar da suka cimma kawo yanzu.288