Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka John Kirby a jiya Alhamis ya bayyana cewa: Hanya daya tilo da zai kawo karshen takaddamar da ke tsakanin kasashen Indiya da Pakistan ita ce jami'an kasashen biyu su hanzarta komawa kan teburin tattaunawa da nufin warware duk wani sabani da ke kaninsu ta hanyar lumana.
Wannan bayani na ma'aikatar hakokin wajen Amurka ya zo ne bayan da jami'an kasar Indiya suka bada sa'o'i 48 ga wani jami'in diflomasiyyar Pakistan kan ya bar cikin kasarsu bayan da suka zarge shi da gudanar da ayyukan leken asiri.288