Daga cikin jimillar ‘yansanda 12,801 da aka dakatar, harda manyan hafsoshi ko shugabannin ‘yansanda kamar 2,500, a cewar wata sanarwar gwamnati da aka fitar.
5 Oktoba 2016 - 12:18
Lambar labari: 783561
Jiya ‘yan sandar kasar Turkiyya sama da dubu 12 aka dakatar daga aiki saboda alakar da akace suna da ita da Fetuhullah Gulen, shaihin malamin nan na kasar Turkiyya wanda aka zarge shi da kitsa makircin yunkurin kifarda gwamnatin kasar a cikin watan Yulin da ya gabata.