24 Faburairu 2016 - 14:51
Nijeriya Da Kamaru Sun Jaddada Aniyarsu Ta Ci Gaba Da Fada Da Boko Haram

Kasashen Nijeriya da Jamhuriyar Kamaru sun sake jaddada aniyarsu ta fadada fadar da suke yi da kungiyar ta'addancin nan ta Boko Haram har sai sun ga bayanta.

Kasashen biyu sun bayyana hakan ne a yayin tattaunawar da ministan cikin gidan Nijeriya Abdurrahman Bello Danbazau yayi da takwararsa na kasar Kamarun René-Emmanuel Sadi dangane da yadda za a yi 'yan kwaskwarima ga tsare-tsaren da kasashen biyu suke da shi na kawo karshen kungiyar Boko Haram din a kasashen nasu da ma yankin baki daya.

Minista Rene Emmanuel Sadi ya ce ministan cikin gidan na Nijeriya ya zo Kamaru din ne don tattauna hanyoyin da za a bi wajen karfafa aiki tare tsakanin kasashen biyu don fada da annobar Boko Haram din, yana mai cewa rashin tsaro da ayyukan ta'addanci wani babban kalubale ne ga kasashen biyu da ke bukatar hada karfi waje guda don fada da shi.

Tun dai bayan rantsar da sabuwar gwamnatin Muhammadu Buhari ta Nijeriyan, gwamnatin ta sanar da aniyarta ta hada kai da kasashen makwabta wajen fada da kungiyar Boko Haram din, wanda kuma ya zuwa yanzu a cimma wasu nasarori a wannan bangaren.288