Mutanen wadanda ba a san ko su wane ne ba sun kai harin ne a ranar Laraba a sansanin sojojin shiga tsakani na majalisar dinkin duniya da ke kusa da Gao a Malin.
A sanarwar da rundunar ta bayar, wadda ta ce motar maharan ta tarwatse ne a kofar shiga sansanin sojin, ta ce daga cikin sojoji 16 da suka ji raunaku, tara na Nijar ne.
A watannin da suka gabata sojojin Nijar tara ne da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a Malin suka mutu a kwantan baunar da aka yi musu.ABNA