Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S}-abna-kasashen hadin gwiwa a karkashin jagoranci kasar Saudiya sun kaddamar da harin soja akan kasar Yaman, kasashen wanda suka hada da Kuwait, Emarat, Jodan,Katar,Saudiya tare da goyon bayan kasar Amurka.
Ruhotanni sunce an kai hare-haren ne a yankuna da daman a kasar musamman babban birnin kasar wato San’a.
Kama ya zuwa yanzu mutane da dama sun rasa rayukan su inda wasu kuma suka jikkata.ABNA