MA’ANAR AL-MILAL WAN NIHAL Milloli da Aqeedu wato kenan AL-MILAL WAN-NIHAL a larabci Malamai suna cewa MILLA ma’anar ta shine kamar DARIQA wato kenan hanya wadda ake dauka daga wasu.Wadda iyakad da’iran daya shafemu shine MILLA a addini. Namu mu anan tana da dangantaka da addini duk da yake tana da bambanci a wasu wurare da kila zamu yi bayani akai.Daya daga cikin ma’anar ta suna cewa Addini shine Da’a wato biyayya. Kenan ita Millah ba a jingina ta zuwa ga daidaikun mutane ko mabiya Annabawa masalan.Sannan ba a jingina ta zuwa ga Allah {T} ba, ko kace MILLATULLAH masalan,ko kuma kace MILLATU ZAID amma ana jingina ta zuwa ga wadanda suka zo da saqonni in ana magana a da’iran addini kenan.Kamar in da ake cewa:-“MILLATA ABIKUM IBRAHIM”.Sannan muna ji a wani wurin Allah yana cewa:- “INNIY TARAKTU MILLATA QAUMIN”. ME AKE NUFI DA NIHLAH Sannan abinda ake cema “NIHLAH” a wata ma’ana itama tayi kama da addini amma bambamcin ta da Addini da Aqida shine cewa akanyi amfani da ita a Aqidu wadanda suke batattu wato bana gaskiya ba wadanda suke ba daidai ba.Sannan ita kanta kalman AQIDA din itama addini ce amma da ma’anar abinda mutum ya qulla.Asalinta shine hada gyaffan ababe wato a dakko wannan gefen da wancan gefen a hada,daga nanne aka samo kalmar AQIDA wato kenan abinda mutum ya qudirta ya qulla acikin zuciyar shi na imani kowanne irin imani ne kuwa wannan saboda haka kenan bahasin da za muyi akan MILLOLI DA AQIDU shine kamar yadda ta bayyana cewa AQIDA kuma ba tare da la’akari da cewa Aqidun na gaskiya ne ko bana gaskiya ba,wannan a mafi yalwan da’ira kenan.Amma musamman akan Aqidun shi’a kenan in kana so ka iyakance iyakan da’iran bahasin mu zaiyi wuya domin yana da yawan gaske. AQIDA mukace duk da yake a baya munyi bahasi akan wasu Aqidu din,kamar Ahlul-Hadith a wannan munyi bincike ne akansu. Sannan munyi bincike akan Aqidun Hambalawa da Ash’arawa,da kuma wani sashi na Mu’utazila da Matturidiya. Saboda haka wannan bahasi ba bahasi bane wanda yanzu muka fare shi,munyi da yawa yanzu muna so mu cigaba ne amma da wannan tarkizi akan Aqidun Shi’a.Yawancin Malamai a da sukan ba kowanne ilimi ilimi maudu’i sai su iyakance maudu’in ilimin.To yanzu muna cewa menene maudu’in wannan ilimin?Yawancin malamai sukan cema maudu’in kowanne ilimi:-“AL- JAMI’UL KULLIY”wato maudu’in kowanne ilimi shine wannan maudu’in wanda ya tattaro kowanne ilimi dake da dangantaka a cikin da’iran wannan ilimin. Wani abu guda daya daza kai ishara zuwa gare shi a cikin wannan ilimin wanda shi yana wakiltan dukkan maudu’an ilimin. To wannan shine maudu’in wannan ilimin,shine ake kira da AL –JAMI’U AL-KULLY. A nan bari ince ba wazifa ta bace a kowani lokaci in na fadi wata kalma sai na zo nayi bayanin ta kwatankwacin ta a hausa,wazifa ta itace inyi bayanin ISDILAHOHI,wazifar mutum itace ya koya ya sani.Zan iya cewa AL-JAMI’UL KULLY a hausa shine wanda ya tattaro maudu’ai gama gari amma bai zama wajibi a kaina inyi haka a kowanne lokaci lokaci ba,tunda darasi ne wannan. Misali nake so in bayar, menene maudu’in ilimin NAHWU?Sai kace maudu in ilimin NAHWU shine wannan maudu’in wanda ya tattaro dukkan mas’alolin da aka tattauna a maudu’in ilimin na NAHWU din.Masalan, idan kace:- AL-FA’ILU MAR FU’UN, AL- MAF’ULU MANSUBUN. AL- FI’ILU MABNY. AL- HAAL MANSUBUN. Misali kenan,in ka dubi wadannan jumlolin da muka fadi yanzu cewa FA’ILU rufu’a ake mashi, MAF’UL ana mashi nasba ne, FA’IL kuma shi ginanne ne akan haraka guda daya, HAAL kuma nasaba ake mai.In ka kalli wadannan dukkansu mas’alolin ilimin NAHWU ne. Amma in ka kalle su kowanne daya bayan daya zaka ga maudu’in wanda ka rattaba wani hukunci akanshi.Misali Al-fa’ilu sai kace maudu’i ne,Marfu’un shine hukuncin da aka rattaba ko aka dabbaqa akan wannan abin da ka kira kace Al-fa’il. Inka kalli kowanne daga ciki zaka ga cewa kalmomi ne{ Al-fa’il} kalma ce, {Marfu’un} kalma ce.Inkace { Al-fi’ilu} itama kalma ce ko ba alura ba ? { Al-hal} itama kalmace koba kalma bace ? itama kalma ce.Saboda haka sai kace maudu’in ilimin NAHWU shine kalma sanan harafin karshe a cikin kalma din.kenan menene maudu’in ilimin NAHWU? Shine kalma. Haka kuma inkace menene maudu’in ilimin USULUL FIQH?Misali,to sai kace maudu’in ilimin USULUL FIQH akan asasin wannan qa’idan AL-JAMI’UL KULLY wato wannan maudu’in wanda ya tattaro dukkan maudu’ai da suke da dangantaka da mas’alolin ilimin USULUL FIQHI.Wannan shine da yawa daga cikin Malamai suka so su iyakance amma sai suka ce shine “ AL-ADILLA AL-ARBA’A”. Gasu kamar haka;- 1 AL-KITAB(ALQR’AN) 2 AS- SUNNAH 3 AL- AQLU, 4 AL,-IJMA. Akan asasin qa’idojin USULUL FIQH na Imamiyah kenan.Idan ka dubi wannan ta’arifin akan cewa shine maudu’in ilimin USULUL FIQH sai ka ga yana da taqaituwa sosai da ma’anar cewa akwai wasu abubuwa masu yawan gasken gaske da zaka ga cewa ya kamata ace sun shiga cikin maudu’in ilimin USULUL FIQHI din amma basu,wadanda suke su ba {KITAB} bane kuma ba{SUNNA} bace sannan kuma ba {AQAL} bane kuma ba { IJMA} bane. Misali kamar abinda ake cema:-“AL-ISTIL ZAMATUL AQLIYYAH” da ma’anar “WUJUBUSH SHAI’I YASTALZIMUL WUJUBA MUQADDIMATIHI,”wannan “Yastalzimu” wato in abu ya wajaba to wannan wajibci din yana wajabtar da wajabcin muqaddima dinshi. Wannan ba abin da muka fadi ba KITAB bane,ba SUNNAH bane kuma AQAL bane sannan ba IJMA bane, wannan abin da muka fadi hukunci ne, ko al wujub?? Musamman in muka tafi akan asasin makarantar Shahidur Sadar wanda yake cewa;- KITABAT din littafi su akan kansu basu bane Hukumush Shar i.Hukumush Shar’i, shi MAD LUL NE NA KITAB. Wannan ma bai wajaba akaina sai nayi bayani dalla dalla ba.Kenan hukunci shi Madlul ne na Dalil wato AL-ADILL AL-ARBA’A, amma shi akan kanshi baya daga cikin AL-ADILLAH AL- ARBA’A wannan daya kenan. Sanan sun tafi akan kamar ace AL-AMARAT ko KABARUTH THIQAH wato labarin da amintacce yake badawa kamar ZURARA.A masali ZURARA yazo yace maka Imam kaza yace kaza sai ya zama yanzu muna bahasi akan cewa idan mutum Thiqa kamar ZURARA ya bada labari, to akwai hujja acikin labarin siqa? Wannan mas’alace daga cikin masa’il na USULUL FIQH ko ba mas’ala bace?Mas’alace, wato kenan Hujjiyah. Dazu muna magana akan Hukum muka ce Hukum shi Madlul ne na kitab amma ba shi bane kitab.To yanzu hujja fa? Hujjiyah,Hujjiyatu kabaruth thiqa. Shi kitab ko ita kitab ce? A’a,. Sunnah inkace a,a, inkace fadin Zurara ai shine Sunnah, sai muce maka abadan ba haka bane.Sunnah itace fadin Ma’asum da aikin Ma’asum da tabbatarwan Ma’asum. Ee, duk da Ma’asum yace mana SADDIQUTH THIQAH ma’ana ku gasganta amintacce,shi wannan daban ne, wannan din shine sunna wato SADDIQU ATHTHIQAH. Shi wannan sunan shi wa? Sunan shi Sunnah. Amma HUJJIYATU KABARUTH THIQAH,idan Thiqah yayi magana muna so mu tabbatar da cewa labarin shi hujja ne ko ba hujja bane? To wannan sunnah ne ? Abadan wannan ba sunnah bane. Sannan Hudur da Zuhur na kalmomi da laffuzan da suka afku acikin nassosi wato “HUJJIYATUZ ZUHUR AL-URFI” cewa idan naga jumlah a ayan Al-qur’ani ya halasta min inyi amfani da ita a ma’anar da na fahimta daga zahirin tarkibin wannan jumlar ko bai halasta ba?Wato kenan zuhur hujja ne koba hujja bane? Masalace daga cikin masa’il na USULUL FIQH ko ba mas’ala bace? ZUHUR mas’alace.To amma ZUHUR din nan da muke Magana akai KITAB ne ko AQAL, ko SUNNA, ko IJMA, ? duk ba daya. Shiyasa wasu daga cikin malaman USUL suka ce to kenan, USULUL FIQH bai da maudu’i, wasu kuma suka ce ba DARURA bane ya sami MAUDU’I guda daya, yana iya samun MAUDU’AI masu yawa. To sai Shahidus sadar yazo yace ba haka bane USULUL FIQH yana da maudu’i, amma maudu’in shi shine:-“AL-ADILLAH AL-AR BA’A”wato Dalil.Ma huwad Dalil?Shine maudu’in USULUL FIQH. Kada ka haddade shi, daya biyu uku, ila akirihi. Kenan meye maudu’in USULUL FIQH a gurin Shahidus Sadar? A wurin shi shine Dalil ko kace Al-adillah.Inka fahimci wannan to menene Maudu’in Al-milal wan-nihal? Akan asasin abinda muka gabatar saboda mu haddade abin da muke so muyi bincike akanshi A darasi na gaba zamu yi bayani akan maudu’in Al-milal wan-nihal da sauran bayanan darasin.Mu hadu a darasi na gaba.ABNA
28 Faburairu 2015 - 12:22
Lambar labari: 673827
Na Shaik Hamzah Muhammad Lawal A’uzu billahi minash shaidanir rajeem. Bismillahir Rahmanir Rahim. Wasallallahu ala Muhammadin Wa Alihid Dayyibinad Dahireen. Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatu.