Kakakin hedkwatar tsaron Manjo Janar Chris Olukolade ya ce sojoji sun gano babura da ko dai aka lalata, ko kuma mayakan kungiyar suka gudu suka bari a garin.
Janar Olukolade ya ce an yanki soja daya da wuka, sannan an harbi wani a lokacin da sojojin suke binciken gano mayakan kungiyar da suka boye.
Ya ce ana gudanar da bincike akan wasu mutane da suka ce su mazauna garin Baga ne, domin tabbatar da cewa ba aiki suke yiwa kungiyar ta Boko Haram ba.ABNA