A watan da ya gabata, an samu karin fadace-fadace a arewacin kasar inda, 'yan gwagwarmayar Islama da mayakan Abzinawa 'yan aware ke fafutukar kama iko tun lokacin da aka rasa tartibiyar gwamnati bayan juyin mulkin da aka yi a Malin a 2012.
Majalisar dinkin duniya da kasar Algeria da ke karbar bakuncin zaman tattaunawar, suna fargabar cewa rikicin zai iya kawo nakasu ga shirin zaman lafiyar.ABNA