Wannan ne dai karon farko da Boko Haram ta kaddamar da hari a Jamhuriyyar Nijar da ke makwabtaka da Najeriya.
Jami’an leken asirin Amurka sun ce Boko Haram ta fara shan wahala saboda taron dangi da dakarun Chadi da Kamaru da Nijar da Najeriya ke yi wa kungiyar.
Sai dai kuma Jami’an leken asirin sun ce Mayakan na Boko Haram babbar barazana ce ga dakarun Najeriya saboda makaman da suka kwasa a garin Baga.
A ranar Litinin ne dai Majalisar Nijar ake sa ran za ta kada kuri’ar amincewa a tura dakaru domin yakar Boko Haram a Najeriya.ABNA