Jelar Jirgin tana dauke da bakin akwati da ke kunshe da na’urorin sadarwar jirgin. Kuma samun jelar zai taimaka wa masu aikin binciken jirgin gano dalilin hatsarin.
Gawawwakin mutane 40 aka tsamo daga tekun Java amma ana tunanin sauran fasinjan jirgin suna can makale a gangan jirgin.
Jirgin ya tarwatse ne a Teku dauke da mutane sama da 160 akan hanyrsa daga garin Surabaya na Indonesia zuwa Singapore.ABN