22 Disamba 2014 - 17:45
Bam ya fashe a kasuwar Bauchi

Wani abu da ake zaton bam ne ya fashe a babbar kasuwar garin Bauchi a arewacin Nigeria.

Kawo yanzu babu cikakkun bayanai game da harin, amma dai rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a lokacin da mutane ke hada-hada.

Harin bam din a kasuwar Bauchi na zuwa ne sa'o'i kadan bayan harin bama-bamai biyu a tashar motoci a Gombe inda mutane 20 suka rasu.

Kungiyar Boko Haram ake zargi da kai wadannan harie-haren, ganin cewar ta kashe dubban mutane a Nigeria.