A cewar Yoweri Museveni, ICC kotun kasashen Yamma ce, kuma zai gabatar da wata shawarar ficewa gaba daya a taron Kungiyar Tarayyar Afirka na gaba.
Mista Museveni ya fadi hakan ne bayan da kotun ta janye tuhume-tuhumen aikata laifukan cin zarafin bil-Adama da ake yi wa shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta, amma ta ci gaba da tuhumar mataimakinsa, William Ruto.
Ya kuma ce bai dace ba a tuhumi shugabannin kasashen Afirka ko mataimakansu.ABNA