A hudubar sallar juma’arsa ta yau a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran: Ayatullahi Muhammad Imami Khashani ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta dogara ne da koyarwar Musulunci da goyon bayan al’ummar Iran da na Jagoran juyin juya halin Musulunci a fagen mallakar fasahar makamashin nukiliya na zaman lafiya, don haka ya zame dole a kan kakashen yammacin Turai su dauki matakin kawo karshen takaddamar da suke yi da kasar ta Iran kan shirinta na makamashin nukiliya saboda ba zasu taba cin nasarar durkusar da shirin ba.
Ayatullahi Imami Kashani ya kara da cewar tawagar Iran a zaman tattaunawa da gungun manyan kasashe biyar gami da kasar Jamus na 5+1 ta tabbatar wa duniya cewar Iran bata da wani shirin mallakar makamin nukiliya, kuma tsari na hankali ya haramta mallakar makamin na nukiliya.ABNA.