4 Nuwamba 2014 - 09:23
Taron Ashura A Najeriya

Cibiyar Mu'assasar Thaqafar Thaqalayn da ke Kaduna ta gudanar da taron tunawa da ranar Ashura ranar litinin 3 ga November 2014


Taron ya fara misalin karfe hudu na yamma agogon Nigeria ,bayan bude taron da addua daga Mal Habibu Zaria, sai kuma Shaik Ibrahim Adam Almisriy ya karanta Ziyara.
Bayan nan sai aka gabatar da Shugaban Mu'assasar wato Maulana Al-ustazul kabir Shaik Hamzah Lawal domin jawabi game da waqi'ar.
Malam yayi bayanai masu yawa game da ala'amarin gwagwarmayan Imam Husain .
Malam yace Ashura ba ta taqaita akan sanya bakaken kaya ba da kuka da karanta ziyara ba, al'amarin ya wuce nan so ake a dauki darasi shi yasa Imam Husain yace ANA QATILUL IBRA, MA ZAKARANIY MU'UMINUN ILLAS TA'ABAR
Malam yayi kira ga al'umma da su dauki darasin tirjiya da fuskanta azzulumai domin Irin abinda Imam Husain yayi kenan. ABNA