Wasu ganau ba jiyau ba, sun tabbatarawa da kanfannin dilancin labaren Faransa na AFP da cewa sunga takunan yaki sun farmawa bataliyyar tsagerun masu daukeda makamai, yayinda kuma sojojin saman kasar masu biyaya ga janar Haftar ke kaddamarda hare-hare da jiragen sama a yankin dake yammacin kasar. dama tunda farko janar Khalifa Haftar ya sanar a ranar talata nan ta kafar televijin din kasar cewa dakarun sa a shirye suke domin fatatakar 'yan ta'ada ko ina suke a cikin kasar. ABNA
15 Oktoba 2014 - 15:06
Lambar labari: 644571
rahotanni daga kasar Libya na nuni da cewa dakarun dake biyaya ga janar Khalifa Haftar sun kaddamarda wani sabon farmaki domin kwato birnin Benghazi dake gabashin kasar wanda ya fada hannun tsageru masu daukeda makamai tun watan juillin wanan shekarar