12 Oktoba 2014 - 19:04
Shugaban Somalia Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Wani Hari Da Aka Kai A Kan Jirginsa

Shugaban kasar Somalia Sheikh Hassan Mahmud ya tsallake rijiya da baya, bayan da mayakan kungiyar Al-shabab da ke da alaka da alkaida suka yi yunkurin kakkabo wani jirgin sama da ke dauke da shi da tawagarsa.

Rahotanni daga kasar ta Somalia sun ce mayakan na kungiyar al-shabab sun yi yunkurin kakkabo jirgin ne wanda yake dauke da shugaban kasar Hassan Sheikh Mahmud tare da wasu ministocinsa, a lokacin da jirgin ke shirin safka a yankin Barawi wanda aka kwace iko da shi daga hannun 'yan shabab.

 

Wani daya daga cikin 'yan tawagar shugaban kasar ta Somalia ya bayyana cewa, sun isa yankin ne da nufin yin rangadi bayan fatattakar 'yan bindiga, ya ce harba makami mai kakkabo jiragen sama da  mayakan na Al-shabab suka yi, hakan wata manuniya ce kan babban kalu-balen tsaro a kasar. ABNA