8 Oktoba 2014 - 19:11

Rahotanni daga kasar Siriya na cewa ana ci gaba da gagarumin ba ta kashi tsakanin dakarun sa kai na Kurdawan kasar da ‘yan kungiyar ta’addancin nan ta Da’esh ko ISIS a garin Kobani da ke arewacin kasar Siriya. Duk da cewa ‘yan ta’addan Da’esh din sun shigo garin to amma har ya zuwa yanzu ba su sami damar kwace shi gaba daya ba sakamakon gagarumar turjiyar da suke fuskanta daga wajen Kurdawan.

Matsalar Kurdawan da kuma wannan gari na Kobani ta fara daukan hankula ne bayan da hadakar kasashen da Amurka ta kirkiro da sunan fada da kungiyar Da’esh suka fara kai hare-hare ta sama kan cibiyoyin ‘yan kungiyar ta Da’esh a yankunan da suke kewaye da garin Kobanin, lamarin da ya share wa ‘yan kungiyar ta’addanci isowa har zuwa bakin garin na Kobani. Ko shakka babu hakan ya kara sanya alamun tambayoyi kan wadannan hare-haren da Amurka da kawayen nata suka kaddamar kan ‘yan Da’esh din, da cewa idan har da gaske ake yi, to ya ya aka yi ‘yan Da’esh suka sami karfin isowa bakin wannan gari har ma da kafa hemomi da sansanoninsu a wajen?

 

Ko shakka babu irin rikon sakainar kashin da kasashen yammaci da sauran kawayensu na larabawa masu ikirarin fada da kungiyar ta Da’esh suka yi wa wannan lamari na garin Kobani ya sanya mutanen garin da ma makwabtansa cikin mawuyacin hali da kuma fadawa cikin hatsarin kisan rashin imani na ‘yan kungiyar ta’addancin ta Da’esh.

 

To sai dai babban abin mamaki da kara sanya alamun tambayar cikin dukkanin wannan lamari shi ne irin matsayar da kasar Turkiyya, wacce ta ke makwabtaka ta kut da kut da wannan yanki na Kurdawa ta dauka. Cikin ‘yan kwanakin da suka gabata gwamnatin Turkiyyan ta jibge tankunan yakinta a kan iyakar kasar da kasar Siriya cikin shirin ko ta kwana na yaki, to sai dai babban abin mamakin shi ne yadda sojojin Turkiyyan suka zuba ido kawai suna ganin abin da ke faruwa a wannan garin ba tare sun yi wani kokari na taimakonsu a fadar da suke yi da ‘yan ta’addan ba. Alhali kuwa a makon da ya wuce ne gwamnatin Turkiyyan ta bukaci majalisar kasar da ta ba ta izini da ikon amfani da karfin soji hatta a wajen kan iyakar kasar da nufin fada da kungiyar ta Da’esh, kuma majalisar ta amince  da hakan. Kamar yadda kuma kwanaki uku zuwa hudun da suka gabata ne firayi ministan Turkiyya Ahmad Dawud Oglo ya ce gwamnatin Turkiyyan ba za ta taba bari wannan gari na Kobani ya fada hannun ‘yan Da’esh ba. To sai dai har ya zuwa babu wani  yunkuri na fada da Da’esh din da aka gani daga wajen gwamnatin Turkiyya ba, face ma dai kara share fage ga ‘yan kungiyar Da’esh din na kama wannan gari.

 

Irin wannan matsaya da Turkiyyan ta dauka ne ya sake tabbatar da abin da wasu masana suka sha fadi na hannun da kasar Turkiyya take da shi wajen kirkiro kungiyar ta Da’esh da kuma share mata fagen aikata ayyukan ta’addancin da take yi a Siriya da Iraki. Don kuwa ko ba komai ba a ga wani abu a kas ba dangane da ci gaba da ihu bayan hari da Turkiyyan take yi na cewa tana fada da ta’addanci, face dai abin da kawai ake iya gani shi ne cewa akwai wata manufa ta daban ta Turkiyyan take son cimma a kasar Siriyan wadda ita ce ganin bayan gwamnatin kasar kamar yadda maganganun da firayi ministan Turkiyya Ahmad Dawud Oglo yayi a wata hira da ya yi da tashar talabijin din nan ta CNN ta Amurka suke tabbatar da hakan inda  ya ce sharadin Turkiyya na shiga wannan yakin shi ne tabbatar da gagarumin sauyi na siyasa a  kasar Siriya, don haka ne ma ya gabatar da batun samar da wani yanki da za a hana jiragen yakin Siriya shawagi a wajen wanda hakan zai ba wa gwamantin Turkiyya cin karenta ba babbaka a yanki da kuma sanya ido kan duk wani yunkuri na Kurdawan kasar Siriyan.

 

A saboda haka ne masana suke ganin shiru da kuma halin ko in kula da gwamnatin Turkiyyan take nunawa mummunan yanayin da Kobanin ke ciki, wani abu ne da ke tabbatar da cewa babban abin da ya dami ‘yan siyasar Turkiyya shi ne yadda za su sami damar da suka samu wajen biyar wannan bakar aniya ta su ta kifar da gwamnatin Siriyan da kuma mayar da Kurdawan kasar karkashin ikonsu. ABNA