25 Satumba 2014 - 15:26
Najeriya : An Dade Da Kashe Abubakar Shekau, Shima Mai Ikirari Da Sunan Sa An Kashe Shi

Sojojin Nigeria sun tabbatar da cewa, sun dade da kashe mutumin da ake zargin shi ne madugun 'yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, A taron manema labarai A birnin Abuja

kakakin rindinar sojan kasar Chris Olukolade ya ce, Wanda ke ikirari da sunan Abubakar Shekau a cikin faya-fayen bidiyon da kungiyar ta kan fitar, sunan shi Mohamed Bashir kuma an kashe shi yayin wani fada a garin Konduga dake arewa maso gabashin kasar, amma lallai shugaban nasu mai suna Shekau sun dade da kashe shi ba tareda bayana rana ko kuma locacinda akayi hakan. Wanan dai shine karon farko da rindinar sojan Najeriya ta bayana mutuwar madugun na Boko haram a hukumance, sabanin cen baya da wasu majiyoyin tsaro suka bayana kashe Shekau din har sau biyu. Yayin taron manema labaran rindinar sojan Najeriya ta nuna faifan bidiyo fadan da akayi a garin Konduga dake jihar ta Borno wanan ya nuna gawawakin mutane da dama cikin filayen garin, inda aka nuna cikin gawawakin huskar mutinan mai ikirarin shine Shekau din, kuma mutinan huskar sa tayi kama sosai da mutunan da yake bayani a cikin faya-fayen bidiyon da kungiyar ta Boko haram ke fitarwa a cen baya wanda suka hada da na inda aka nuna ‘yan matan cibok da kuma na baya-bayan nan. ABNA