A dai bangaren kuwa kungiyar Hizbullahi da ke marawa Bashar Assad baya ta yi kakkausar suka ga wadannan hare-hare.
Shugaban hizbullah sayyid Hasan Nasrallah wanda ke gabatar da jawabi ga magoya bayansa a birnin Beirut, ya ce yana da shakku idan har Amurka da kawayenta sun kai harin ne da niyyar wargaza kungiyar ISIS ko kuma da wata manufar ta daban. ABNA