21 Satumba 2014 - 13:48
Za'a Kafa Gwamanatin Hadin Guywa

A kasar Afganistan yau ne hukumar zabe mai zamen kan ta zata bayana sakamakon zaben shugaban kasar, kazalika a yau din ne ake sa ran ‘yan takara biyu Ashraf Ghani da Abdullah Abdullah zasu sa hannu kan yajejeniyar kafa gwamnatin hadin guywa.

 Kamar yadda kakakin hukumar zaben mai zamen kan ta Noor Mohammad Noor ya shaidawa kanfanin dilancin labarne AFP ya ce yau lahadi hukumar zata bayana sakamakon zaben shugaban kasar na dindin-din. ‘yan takara biyu da suka hada da Ashraf Ghani da Abdullah Abdullah su ne dai ‘yan takara da suka fafata a zagaye na biyu a zaben neman shugabancin kasar ta Afganistan na watan Yuly wanan shekara wanda kuma zasu maye gurbin shugaba Hamid Kharzai. Dukka dai bangarorin biyu sun tabbatar cewa  ‘yan takara sun amunce da sa hannun kan yarjejeniyoyin da suka cimma jiyya assabar domin kafa gwamnatin hadaka, kuma yau zasu sa hannu kan yarjejeniyar da suka dadale.  ABNA