13 Satumba 2014 - 10:09
Shugabannin Rasha Da Iran Sun Jaddada Shirinsu Na Kara Bunkasa Alakar Kasashensu

Shugabannin kasashen Rasha da Iran sun gudanar da wata tattaunawa a gefen taron shugabannin kasashe na kungiyar bunkasa tattalin arziki ta Shanghai wanda aka kammala jiya a kasar Tajikistan.

A yayin ganawar tasu, shugaba Vladmir Putin na Rasha da kuma takwaransa na kasar Iran Sheikh Hassan Raunahi, sun mayar da hankali kan muhimman batutuwa na bunkasa harkokin tattalin arziki da kasuwanci da kuma batutuwa na ilimin kimiyya da fasaha a tsakanin kasashensu.

 

Shugaba Rauhani ya ce alaka tsakanin Iran da Rasha alaka ce ta tarihi wadda ke kara samun bunkasa a kowane lokaci, a nasa bangaren shugaba Putin na Rasha ya jaddada matsayin kasarsa na ci gaba da yin aiki kafada da kafada tare da Iran a bangarori daban-daban, na siyasa, tattalin arziki ilimi al'adu da dai sauransu.

 

Daga karshe shugabannin kasashen biyu sun jaddada muhimmancin yin aiki tare domin fuskantar ayyukan ta'addanci da ke barazana ga dukkanin yankunan gabas ta tsakiya. ABNA