8 Satumba 2014 - 13:44

Kungiyar Alshabab da ke Somalia, ta sanar da nada sabon shugaba, bayan da Amurka ta kashe jagoranta mai suna Ahmed Abdi godane a wani harin da ta kai ma sa cikin makon da ya gabata.

A Wata sanarwa da ta fitar a shafinta na yanar gizo, kungiyar ta Alshabab ta bayyana wani mai suna Ahmad Umar Abu Ubaidah a matsayin sabon shugabanta, kuma majiyoyin kungiyar sun bayyana sabon shugaban a matsayin na hannun damar marigayi Abdi Godane.

Har ila yau a cikin sanarwar, kungiyar wadda ta share tsawon shekaru tana yakar gwamnatin Somalia, ta lashi takobin daukar fansa dangane da kisan da aka yi wa shugabanta, sannan kuma ta jaddada mubaya’arta ga jagoran kungiyar Alka’ida Ayaman Alzawahiri.

Kwanaki da dama bayan harin da jirgin yakin Amurka mai sarrafa kansa ya kai akan shugaban na Alshabab, to amma jami’an kungiyar sun ki fitowa fili su bayyana wa duniya cewa ya mutu, to amma sanarwar nada Abu Ubaidah na mai tabbatar da cewa an kashe shugaban na kungiyar.

Kafin wannan hari na Amurka dai, hukumomi a Magadishiu sun bai wa mayakan kungiyar wa’adin kwanaki 45 su ajiye makansu domin samun afuwa ko kuma su hadu da fushin jam’an tsaron kasar da takwarorinsu na kungiyar tarayyar Afirka wato AMISOM. ABNA