7 Satumba 2014 - 10:15
Ana Ci Gaba Da Barin Wuta Tsakanin 'Yan Bindiga Da Dakarun Soji A Birnin Bengazi Na Libya

Rahotanni daga birnin Benghazi na kasar LIBYA sun ce a jiya an yi barin wuta mai tsanani tsakanin sojojin kasar da ke mara baya ga Halifa Haftar da kuma tsoffin yan tawayen kasar da ke dauke da makamai.

Majiyoyin suka ce an yi ta barin wuta a lokacin da masu dauke da makaman suka kaddamar da hari kan wani wurin tsaro, yayin da sojjin da ke biyayay ga Haftar suka mayar da martani da makaman atilari a kan wasu sansanonin 'yan bindigar, haka nan kuma wasu jiragen yaki masu safkar angulu mallakin rundnar sojin kasar sun yi lugudan wuta a kan sansanin masu dauke da makaman.

 

A nata bangaren sabuwar gwamnatin rikon kwaryar kasar ta Libya ta zargi gwamnatin Sudan da hannu wajen taimaka tsoffin 'yan tawayen na Libya masu tsatsairan ra'ayi da ta kira su 'yan ta'adda, bayan da gwamnatin ta Libya ta ce wani jirgin Sudan ya shigo kasar a jiya dake da makamai, da nufin mika su ga tsoffin 'yan tawayen. ABNA