28 Agusta 2014 - 10:23
An Dage Lokacin Komawar Makarantu Saboda Cutar Ebola

Hukumomin ilimi a Najeriya sun sanar da dage lokacin komawar makarantun boko a dukkanin fadin kasar a wani mataki na dakile yaduwar cutar Ebola.

Ministan ilimi a Najeriya Ibrahim Shekarau, shine ya sanar da hakan yane mai cewar hakan ya shafi 'yan makarantun firamare da na sakandare a dukkanin fadin kasar, a matsayin daya daga matakan da ake dauka na dakile yaduwar cutar Ebola a kasar. Malam Shekarau ya kara da cewa, an dage komawar 'yan makarantar ne ya zuwa ranar 13 ga watan Oktoba mai zuwa, duk da cewa a baya akan bude makarantun ne a mako na biyu na watan Satumba. Ministan ilimin Najeriyar ya kuma bukaci hukumomin ilimi na daukacin jihohin kasar, da su aike da ma'aikatansu da suka samu horo game da jinya a makaratu daban daban domin tinkarar halin ko ta kwana. ABNA