A cikin rahoton da hukumar ta fitar a jiya, ta ce ma'aikatan kiwon lafiya fiye da 240 ne suka kamu da kwayoyin cutar a kasashen Guinea, Saliyo Liberia da kuma Najeriya, ya zuwa yanzu kimanin 120 daga cikinsu sun riga mu gidan gaskiya, sakamakon kurakuran da ake samu wajen yin mu'amala da mutanen da suka kamu da kwayoyin cutar.
A ranar 20 ga wannan wata na Agusta hukumarv lafiya ta fitar da wata kididdiga ta jimmilar mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da kwayoyin wannan cuta har zuwa ranar fitar da rahoton, inda ta ce adadin ya kai mutane 1427, kasar Liberia ce kan gaba da mutane 624, sai kuma Guinea da mutane 406, sai saliyo da mutane 392, yayin da a Najeriya kuma mutane 5 suka rasa rayukansu. ABNA