A bayanin hadin gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya da Hukumar Lafiya ta Majalisar “WHO” suka fitar a jiya Asabar sun bayyana shirinsu na aikewa da duk wani kayan aiki gami da na’urori da suka dace zuwa kasar Liberiya domin yaki da cutar zazzabin Ebola mai saurin kisa da ke ci gaba da yaduwa a sassa daban daban na kasar.
Keiji Fukuda mataimakin shugaban Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya “WHO” ya bayyana cewa a halin yanzu haka tuni suka bude wata cibiya da ke kula da mutanen da suka kamu da cutar ta Ebola a gefen birnin Monrovia fadar mulkin kasar.
A halin yanzu haka dai kididdiga ta tabbatar da cewa cutar ta Ebola ta lashe rayukan mutane 1,427 a wasu kasashen da suke nahiyar yammacin Afrika da suka hada da Guinea Conakry, Saliyo, Liberiya da Nigeriya. ABNA