Amano ya zo kasar Iran ne don ganawa da jami’an gwamnatin kasar kafin taron tattaunawa tsakanin Iran da manya manyan kasashen duniya a ranar 25 ga watan Augusta da muke ciki kan shirinta na makamashin nuclear.
Har’ila yau shugaban hukumar ta IAEA ya gana da shugaban kasar Iran Dr Hassan Ruhani don fayyace masa matsayin hukumarsa a kan tattaunawa da kuma sanin irin jawaban da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta shirya kan tambayoyin da hukumar ta bukaci amsoshinsu daga wajenta. ABNA