22 Yuli 2014 - 18:18
Jonathan ya gana da iyayen 'yan Chibok

Bayan kusan kwanaki 100 da sace 'yan mata dalibai a Chibok, shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya gana da iyayen 'yan matan da aka sace.

Dalibai 51 da suka kubuce daga hannun 'yan Boko Haram da kuma iyayen yara fiye da 100 ne suka halarci ganawar a fadar Shugaban Nigeria da ke Abuja.

A makon da ya gabata ne iyayen yaran suka kauracewa ganawa da Mr Jonathan bisa wasu batutuwa na rashin fahimtar juna.

Mr Jonathan na shan suka saboda rashin ganawa da iyayen yaran tun farko da kuma batun rashin hobbasa a kokarin ceto 'yan matan da aka sace tun a watan Afrilu.

Kungiyar Boko Haram wadda ta sace 'yan matan fiye da 200 ta ce za ta iya musayarsu da mayakanta da ake tsare da su a gidajen yarin Nigeria.

Rikicin Boko Haram ya raba mutane dubbai da muhallansu a yayinda wasu rahotannin suka ce kungiyar ta kafa tutocinta a wasu sassan jihar Borno. ABNA