28 Mayu 2014 - 15:16
Gumurzu Ya Lashe Rayukan 'Yan Kungiyar Al-Shabab Da Na Al'ummar Wani Kauye A Somaliya

Kimanin mutane 40 ne suka rasa rayukansu a wani dauki ba dadi da aka yi tsakanin al’ummar kauyen Aato da mayakan kungiyar Al-Shabab ta masu tsaurin ra’ayin addinin Islama a kasar Somaliya.

Gwamnan lardin Bakool da ke kasar Somaliya Muhammad Abdi Tall ya sanar da cewa; A safiyar jiya Talata mayakan kungiyar Al-Shabab ta masu tsaurin ra’ayin addinin Islama sun farma kauyen Aato da ke karkashin lardinsa kusa da kan iyaka da kasar Habasha, inda al’ummar kauyen suka mayar da martani domin kare kansu lamarin da ya janyo hasarar rayukan mutane kimanin 40 a tsakanin bangarorin biyu.

Abdi Tall ya kara da cewa; Gumurzun ya lashe rayukan mutanen kauyen na Aato 27 tare da mayakan kungiyar Al-Shabab 12, kuma al’ummar kauyen na Aato sun samu nasarar fatattakan ‘yan ta’addan kungiyar ta Al-Shabab daga kauyensu.ABNA