27 Mayu 2014 - 09:34
Marocco Ta Kame Wasu Mutane 2 Masu Safarar Matasa Zuwa Kasar Siriya

Gwamnatin Marocco ta cafke wasu Mutane guda 2 kan zarkinsu da safarar Matasa zuwa kasar Siriya. A jiya litinin Ma'aikatar cikin gida ta kasar Marocco ta bayyana cewa jami'an kasar sun kame wasu Mutane guda 2 wadanda suke da hannu wajen tura Matasa zuwa kasar Siriya don yaki da Gwamnatin basher Al'asad

Gwamnatin ta kara da ce wadannan Mutane da aka kama sun tabbatar da cewa suna tura matasan Maraccon ne zuwa kasar Turkiya inda daga can a kwai wasu Mutane na daban wadanda suke isa da su zuwa kasar ta Siriya.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa daga fara rikici a kasar ta Siriya a shekara ta 2011 miladiya fiye da Matasar Marocco dubu guda ne suka je kasar Siriya don taya 'yan ta'addar Sirya yakar Gwamnatin basher Al'asad inda Gwamnatin Rabat ta sha nanata cewa tana iya kokarinta na ganin ta rusa duk wata kungiyar mai yin safarar Matasan zuwa kasar Siriya.

Matasan da aka yaudara , kafin su dawo kasar su sun bukaci Gwamnati da ta yi masu afuya a wata wasika da suka rubuta mata saidai Gwamnatin ta Rabat ba ta gamsu da bukantun na su ba, inda bayan sabkarsu a filin sabka da tashi na jiragen saman brnin Rabat jami'an tsaron kasar sun cafkesu inda aka yanke masu hukuncin shekaru uku a gidan yari.ABNA