An yi ta kiraye-kiraye ga 'yan kasar ta Masar da su fito su kada kuri'unsu don maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.
Sai dai kungiyar 'yan uwa musulmi da Jam'iyar tsohon shugaba Mohammed Morsi da aka tumbuke a bara, ke kan gaba wajen yin kiran a kauracewa zaben.
Haka ma wasu dumbin matasa masu ra'ayin juyin juya hali na neman jama'a su nisanci rumfunan zaben.ABNA