18 Mayu 2014 - 16:26
Akalla Mutane 79 Sun Mutu A Rikicin Bengazi Na Kasar Libiya

Rahotanni daga kasar Libiya sun bayyana cewar alal akalla mutane 79 sun rasa rayukansu sannan wasu sama da 141 kuma sun sami raunuka sakamakon barin wuta mai tsanani d ya abku tsakanin dakaru masu biyayya ga tsohon Janar Khalifa Haftar da na wasu kungiyoyi masu tsaurin ra’ayin addini a garin Bengazi da ke gabashin kasar.

Ma’aikatar lafiya ta kasar Libiyan ce ta sanar da hakan inda ta ce tuni aka garzaya da wadanda suka sami raunukan zuwa wasu asibitoci 5  yankin don yi musu magani.

Gwamnatin kasar dai ta zargi Janar Haftar, wanda ya taka rawa wajen kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Mu’ammar Gaddafi da kokarin shirya juyin mulki da kifar da gwamnatin tana mai shan alwashin kawo karshen wannan rikicin.

A wata sanarwa ta hadin gwiwa tsakanin gwamnati, majalisa da sojojin kasar Libiyan suka fitar sun sha alwashin ci gaba da fada da masu tada fitinar suna masu sanar da hana tashi da kuma shawagin duk wani jirgi a garin na Bengazi da barazanar kakkabo duk wani jirgin da aka ganshi a sararin samaniyar. Wannan barazanar dai ta biyo bayan rahotannin da suke cewa dakarun tsohon janar din sun yi amfani da jiragen yaki wajen kai hare-hare.ABNA