10 Mayu 2014 - 17:03

Babban muftin kasar Saudiyya Sheikh Abdul’aziz bn Abdullah Al Sheikh ya bayyana kungiyar Boko Haram ta Nijeriya a matsayin khawarijawa da suka fice daga tafarkin Musulunci da kuma gudanar da ayyukan da suka bakanta sunan Musulunci bayan sace ‘yan mata sama da 200 da suka yi a garin Chibok na jihar Borno

Jaridar Al-Hayat ta kasar Saudiyya ta jiyo babban muftin yana fadin cewa sace ‘yan mata da kungiyar Boko Haram din ta yi wani aiki ne kungiyar da ta kauce wa tafarkin Musulunci, don kuwa Musulunci yana adawa da sace mutane da zubar da jinin mutanen da ba su ci ba su sha ba.

Yayin da yake magana dangane da sanarwar da shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya yi na aure da kuma aurar da wadannan ‘yan matan da suka sace, Sheikh Abdul’aziz Al Sheikh ya ce wannan auren haramun ne don kuwa ‘yan Boko Haram din ba su da hakkin aurar da su, yana mai cewa wannan abin da ‘yan Boko Haram din suke yi wani shiri ne da aka tsara musu da nufin bakanta sunan Musulunci.ABNA.